Shugaban Kasa Tinubu Ya Tafi Faransa, Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Ya Tafi Kasar Senegal.

Shugaban kasa Tinubu Ya tafi Faransa, Mataimakin shugaban kasa Kashim Ya tafi kasar Senegal.

 

A jiya ne shugaba Bola Ahmed Tinubu zai tashi zuwa birnin Paris na kasar Faransa domin ziyarar aiki.

 

 Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru a cikin wata sanarwa ya ce yayin ziyarar, shugaban zai kimanta ayyukan gwamnatinsa na tsakiyar wa'adi tare da tantance muhimman abubuwan da suka dace Tafiyar wacce zata kasance tsawon mako

biyu.

 

 Da yammacin yau ne mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima Ya Bar Abuja zuwa Dakar, kasar Senegal, domin wakilcin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wajen bikin samun ‘yancin kai karo na 65 a kasar.

 

 Kasar Senegal na bikin ranar samun ‘yancin kai ne a ranar 4 ga watan Afrilun kowace shekara, inda ake bikin ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Faransa a shekara ta 1960. Ranar dai na da alfaharin al’ummar kasar, tare da shagulgula, fareti, da al’adu.

Umar Sani

Journalist

Follow Me:

Comments