Siyasa

Tun Farko Gayyatar Da Shelkwatar ƴansanda Ta Yi Wa Sarki Sanusi Ba Ta Da Amfani - Peter Obi

Tun farko gayyatar da shelkwatar ƴansanda ta yi wa Sarki Sanusi ba ta da amfani - Peter Obi Peter Obi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP), ya yaba wa Rundunar ‘Yansandan Najeriya bisa janye gayyatar da ta aikewa Muhammadu Sanusi, Sarkin Kano. A makon da ya gabata ne, ‘yansanda suka gayyaci Sanusi zuwa hedikwatar rundunar domin yi masa tambayoyi kan zargin kashe-kashe da suka faru a lokacin bikin Eid-el-Fitr da ya gabata. Da yake mayar da martani a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, Obi ya ce hanyar warware matsalar a matakin ƙasa-ƙasa (wato ba tare da tursasawa daga sama ba) zai ƙara kawo zaman lafiya da amincewar jama’a. Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce ba bu buƙatar wannan gayyata tun da farko, kuma hakan na iya tayar da hankali a lamarin da tuni ya ɗauki zafi. “Ina so in yaba wa Rundunar ‘Yansandan Najeriya saboda wannan hukuncin da ta ɗauka cikin hikima a kan lokaci, na janye gayyatar da aka aikewa Mai Martaba Muhammadu Sanusi II,” in ji Obi. “Idan aka yi la’akari da yanayin tashin hankali a cikin al’umma a yanzu, irin wannan gayyata ba ta da wani amfani, kuma tana iya ƙara tayar da hankali a cikin rikicin da tuni ya yi zafi. “Akwai cikakkiyar rundunar ‘yan sanda mai aiki a jihar Kano, wadda ke da ƙwarewa da ƙarfin da za ta iya magance irin waɗannan lamurra a cikin jihar. “Shi ya sa muke da manyan jami’ai masu matsayi irin su Kwamishinonin ‘Yan Sanda da Mataimakan Sufeto Janar na Shiyya (AIGs), domin su rika gudanar da irin waɗannan al’amura a matakin jihohi da shiyyoyi.”

Shugaban Kasa Tinubu Ya Tafi Faransa, Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Ya Tafi Kasar Senegal.

Shugaban kasa Tinubu Ya tafi Faransa, Mataimakin shugaban kasa Kashim Ya tafi kasar Senegal. A jiya ne shugaba Bola Ahmed Tinubu zai tashi zuwa birnin Paris na kasar Faransa domin ziyarar aiki. Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru a cikin wata sanarwa ya ce yayin ziyarar, shugaban zai kimanta ayyukan gwamnatinsa na tsakiyar wa'adi tare da tantance muhimman abubuwan da suka dace Tafiyar wacce zata kasance tsawon mako biyu. Da yammacin yau ne mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima Ya Bar Abuja zuwa Dakar, kasar Senegal, domin wakilcin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wajen bikin samun ‘yancin kai karo na 65 a kasar. Kasar Senegal na bikin ranar samun ‘yancin kai ne a ranar 4 ga watan Afrilun kowace shekara, inda ake bikin ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Faransa a shekara ta 1960. Ranar dai na da alfaharin al’ummar kasar, tare da shagulgula, fareti, da al’adu.

YANZU-YANZU: Natasha Ta Kayar Da Akpabio Da Yahaya Bello A INEC

YANZU-YANZU: Natasha Ta Kayar Da Akpabio Da Yahaya Bello A INEC Hukumar Zaɓe INEC Ta ce Koke-koken a dawo da Sanatar da ke wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya bai cika sharuddan sashe na 69(a) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar alif 1999 ba A don haka hukumar ta ce ta kori koken tare da jaddada sanata Natasha a matsayin halastacciyar sanatar Jihar Kogi ta tsakiya.

Da Dumi Dumi Shugaba Tinubu Zai Yi Makonni Biyu A Sabuwar Ziyarar Aiki ƙasar Faransa, Ya Ce Zai Ci Gaba Da Harkokin Shugabanci Daga Paris

Da Dumi Dumi Shugaba Tinubu zai yi makonni biyu a sabuwar ziyarar aiki ƙasar Faransa, ya ce zai ci gaba da harkokin shugabanci daga Paris. Menene tinanin ku akai

Duk Abinda Ya Sameni , Ododo, Akpabio, Yahaya Bello, Su Ke Ɗaukar Nauyi ~ Natasha

Duk Abinda Ya Sameni , Ododo, Akpabio, Yahaya Bello, Su Ke Ɗaukar Nauyi ~ Natasha Sanata mai wakiltan Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, a ranar Talata, ta ce shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, da Gwamna Usman Ododo, da kuma tsohon Gwamna Yahaya Bello, idan wani abu ya same ta sune da alhakin hakan. Natasha-Akpoti ta ce ya kamata ‘yan Najeriya su dora alhakin wadannan sunayen da aka ambata a sama idan an kai wa mabiyanta hari ko kuma an halakata ko wani cikin mabiyanta.