Mun Shirya Tsaf: Za mu kai Nasiru El-Rufai Kotu ~ Majalisar Kaduna Majalisar dokokin jihar Kaduna ta bayyana shirin daukar matakin shari’a a kan tsohon gwamna Nasir El-Rufa’i bisa zarginsa da kiran mambobinta da cewa “jahilai ne”. ‘Yan majalisar dai sun bayyana kalaman El-Rufai a matsayin na bata suna kuma sun dage cewa sun cika ka’idojin da kundin tsarin mulki ya tanada na rike mukamai.